TAKAITACCEN TARIHIN TASKAR SULTAN MEDIA SERVICES

Taskar Sultan wata kafa ce da aka ƙirƙire ta domin ta faɗakar, ta ilmantar, ta kuma nishaɗantar da al'umma. Ta kuma farantawa jama'a musammanma ma'abota sauraronta a ko da yaushe. 

Taskar Sultan kafa ce da take yaɗa shirye-shiryen ta a kafofin sada zumunta na Facebook, WhatsApp, Instagram, Twitter, YouTube. Kuma babban burin wannan kafa shi ne ta wayar da kan al'umma ta hanyar kawo musu sahihan labarai, tare da kiyaye mutuncin kowa. 

Taskar Sultan an buɗe tane a ranar  7 ga watan Rabi'us Thani a shekara ta 1443 Hijjiriya. Wanda ya yi daidai da 12 ga watan Nuwamba na shekarar 2021 Miladiyya.
A Potiskum a jihar Yoben Najeriya. Tana da ma'aikatan da ba su gaza Ashirin ba. Sannan kuma tana gabatar da shirye-shirye a ranaku kamar haka a cikin mako:

1. Ranar Lahadi;
* Sana'o'i da kasuwanci. 
* Tarbiyar Iyali. 
* Zaman tare. 
* Ilimi hasken rayuwa. 

2. Ranar Litinin;
* Labaran mako. 
* Waiwaye adon tafiya. 

3. Ranar Laraba;
* Lafiya jari. 
* Tarihin shahidan mu. 
* Labaran wasanni. 
* Kunne abin sauraro. 

4. Ranar Jumu'a;
* Sada zumunci. 
* Sharhin jaridu. 
* Wasa ƙwaƙwalwa. 
* Darasi a rayuwar mu. 

5. Ranar Asabar;
* Baƙon mu na mako. 
* Duniya labari. 

Waɗannan sune ranakun da wannan kafa take gabatar da shirye-shiryen ta, lokaci, da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare 8:30pm. Tana kuma ɗora bidiyoyi masu daɗi a channel ɗin ta na YouTube mai suna Taskar Sultan TV.📺 

Muna fatan za ku ci gaba da bibiyar mu, domin sai da ku tayoyin kafar za su ci gaba da garawa. Sannan ku bayyana mana ra'ayoyin ku akan shirye-shiryen da muke kawo muku a e-mail ɗin mu mai suna taskarsultan9@gmail.com.

Sannan za ku iya bibiyarmu a shafinmu na yanar gizo mai adireshi kamar haka www.taskarsultan.com.ng

Post a Comment

0 Comments